‘Yan Bindiga Sun Kashe Limami A Katsina Bayan Ya Ƙi Yadda Su Yi Garkuwa Da Shi

344

‘Yan bindiga a Jihar Katsina sun kashe Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sabon Garin Bilbis sakamakon ƙin yadda su yi garkuwa da shi.

A ranar Litinin ne ‘yan bindigar suka kashe Malam Adam a gonarsa dake wajen garin.

Sabon Garin Bilbis, garin da yake kan iyakar jihar Zamfara da Katsina, yana cikin ƙaramar hukumar Faskari ne a Jihar ta Katsina.

Wani jami’in masallacin, Lawal Mamman, wanda ya sanar da rasuwar malamin, ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu mata da suke yi wa limamin aiki a gonar a lokacin harin.

Lawal ya ce ‘yan bindigar sun buƙaci Malam Adam ya bi su a kan ɗaya daga cikin baburansu amma sai ya ƙi.

“Sai suka fara yi masa barazanar harbi da bindiga amma ya ce ba inda za shi duk da sun ce za su kashe shi. Ya ce musu ƙafarsa tana ciwo saboda haka ba zai iya bin su cikin daji ba.

“Bayan wannan sa-in-sa, sai ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ya ce kawai su kashe shi. Sai suka kashe shi suka bar gawarsa a nan amma suka tafi da matan”, in ji Lawal.

A wani labarin kuma, ‘yan bindiga sun saki mutum 25 da suka yi garkuwa da su kimanin makonni biyu da suka gabata a ƙauyen Kanon Haki, shi ma dai a ƙaramar hukumar ta Faskari.

Wani mutum, Bilyaminu Idris, ya ce akwai ‘yan uwansa mata biyu da wani kawunsa a cikin waɗanda ‘yan bindigar suka saki ranar Litinin.

Sai dai bai ce ko an biya tara ko kuma a’a ba kafin sakin nasu.

Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa, bai ɗaga waya ba lokacin da aka kira shi, kuma bai bada amsa ba ga gajeren saƙo da aka tura masa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan