Zuma Farar Saƙa: Abdulkarim Abdussalam Zaura matashin ɗan siyasar da Kano ta ke buƙata

300

A daidai lokacin da shekarar 2023 ke ƙara matsowa wanda kuma a cikinta ne za a yi manyan zabuka a faɗin Najeriya, kuma tuni masu sha’awar neman kujeru a matakai daban-daban musamman kujerar gwamna ke ta yin shirye-shirye da kuma ƙulla – ƙulla irin ta siyasa domin ganin haƙansu ya kai ga cimma ruwa.

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya wanda nan ne cibiyar siyasar Arewacin ƙasar nan la’akari da irin fitattun ƴan siyasar da su ka fito daga jihar, tuni aka fara ganin fuskokin masu buƙatar gadon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na ta shige da fice wajen ganin sun kai ga gaci.

Alhaji Abdulkarim Abdussalam Zaura

A jam’iyyar APC wacce ita ce ke mulkin Kano da Najeriya akwai masu neman wannan kujera ta gwamnan Kano, sai dai kamar yadda masu iya magana kan ce ko a cikin karfe akwai zinare da azurfa wanda kuma kowa ya sani darajar Zinaren ta ɗara ta sauran.

Babu shakka duk a cikin masu neman buƙatar kujerar gwamnan Kano a cikin jam’iyyar APC babu wanda ya kai Abdulkarim Abdussalam Zaura cancanta da kuma dacewa akan zama gwamnan jihar Kano a shekarar 2023, domin al’ummar jihar Kano shaida ne akan irin ƙoƙarin da A.A Zauran ke yi wajen tallafawa al’umma domin ganin rayuwarsu ta inganta.

Wa Jihar Kano Ta Ke Buƙata?

Haƙiƙa jihar Kano tana buƙatar jajirtaccen matashi wanda ya ke da ilimin addinin Islama da kuma na zamani, wanda ya ke da sanayya tsakanin manyan ƴan kasuwa da ƴan boko da ma’aikatan gwamnati da kuma goyon bayan ƙungiyoyin fararen hula.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Abdussalam Abdulkarim Zaura

Hakazalika Kano tana buƙatar mutumin da zai kawo sauyi a harkar ilimi tun daga matakin Firamare wanda nan ne tushe da kuma inganta kiwon lafiya ta hanyar samar da magani a asibitoci da kuma gina hanyoyi a yankunan karkara, da samar da ayyukan yi ga matasa da baiwa mata nagartaccen jari domin dogaro da kai.

Alhaji Abdulkarim Abdussalam Zaura da Alhaji Aliko Dangote


Jihar Kano tana buƙatar jajirtaccen shugaban da zai samar da ƙananan birane tare da samar da ababen more rayuwa ga mazauna waɗannan yankunan domin hakan zai rage kwararowar mazauna karkarar zuwa birane. Kuma zai bunƙasa harkar noma da kiwo ta hanyar fadada kamfanin samar da takin zamani mallakin jihar Kano wato KASCO, inda manoma za su samu takin a farashi mai rahusa.

Kazalika jihar Kano tana buƙatar mutum mai gaskiya da riƙon amana da kuma sanin ya kamata da zai farfaɗo da aikin gwamnati da raba birnin da tarin shara da magance matsalar daba da ƙananan sace – sace da kuma ƙwacen waya.

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Abdulsalam Abdulkarim Zaura

Tabbas ga duk mutumin da ya san waye Abdulkarim Abdussalam Zaura ya san shi ne jajirtaccen matashin da ya ke da wannan niyyar kuma shi ne zai iya kai jihar ga tudun mun tsira a zaɓen shekarar 2023.

Lallai jihar Kano tana buƙatar mutum mai gaskiya da riƙon amana kuma haziki wanda zai ƙara bunƙasa tare da haɓaka tattalin arzikinta daga inda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsaya, kuma ba kowa bane wannan mutum sai Alhaji Abdulkarim Abdussalam Zaura.

Muhammad Abba ya rubuto daga Kano 08064230122

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan