An gina wa al’ummar ƙauyen Shara dake ƙaramar hukumar Sumaila a Jihar Kano makarantar firamare.
Wannan dai ya sa al’ummar garin cikin farin ciki mara misaltuwa
Ƙauye Shara yana da aƙalla mutum 3000 amma babu ko da mutum ɗaya da ya kammala karatun furamare saboda wahalhalun da suke fuskanta wajen zuwa wata makaranta da ke nesa da garin nasu, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.
Cibiyar Bunkasa Fasarar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma,CITAD, ce ta yi uwa ta yi makarɓiya wajen ganin ginin makarantar ya samu.
Ɗaliban sabuwar makarantar da aka a ƙauyen na Shara sun cika da farin cikin samun sabbin ajujuwan karatu guda biyu da ofishin hedimasta, bayan sun shafe shekaru suna daukar karatu a gindin bishiya, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.
Malam Muhammad Labiru Musa shi ne shugaban kungiyar iyayen yara da malaman makaranta ta Shara, ya shaida wa BBC cewa rashin irin wannan daddadan yanayi na karatu na cikin dalilan da suka hana al`ummar garin mai mutum fiye da dubu uku yin karatun zamani, don haka babu ko da mutum daya da ya kammala furamare.