Kotu ta bayar da umarnin tsare Mu’az Magaji a gidan yari saboda aikata laifin ɓata suna

1228

Wata kotun Majistare ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Sari’a Aminu Gabari ta bayar da umarnin tsare wani ɗan jam’iyyar APC mai suna Mu’azu Magaji Danbala a gidan gyaran hali bisa zarginsa da bata sunan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ƴaƴaansa Abdulaziz Ganduje da Balaraba Ganduje.

Jaridar Justice Watch News ta ruwaito cewa an gurfanar da mutanen biyu a gaban kotun bisa zargin haɗa baki, cin zarafi, tayar da hankulan jama’a da ɓata sunan wani wanda ya saɓawa sashi na 97, 114, 391 da 399 na kundin laifuffuka.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje

Tun da farko shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Auwal Lawal Shu’aibu ne ya shigar da ƙarar gaban kotun, inda ya ambaci sunayen Mu’azu Magaji Ɗanbala da Jamilu Shehu dukkanin su daga ƙaramar hukumar Ƙiru ta jihar.

Waɗanda ake zargin dai sun ƙi amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa, inda daga nan ne lauya mai kare waɗanda ake tuhuma ya nemi a bayar da belinsu.

Kotun dai ta ƙi amincewa da bayar da belin wanda ake zargin bayan da lauyan masu shigar da ƙara Barista Wada Ahmad Wada, Babban Lauyan gwamnati ya ƙi amincewa da buƙatar belin.

Alkalin kotun, ya umarci hedikwatar ƴan sandan da ke sa ido kan manyan laifuka (SCID) da ta gabatar da kundin da ta ke tattara bayanai domin kotu ta yi duba gareshi kafin ta yi nazari kan yiwuwar bada shi beli ko sabanin haka.

Sai dai alkalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba don ci gaba da sauraro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan