Mun Mayar Wa Gwamnatin Tarayya Rarar Kuɗi Har Biliyan N3.51— JAMB

370

JAMB Ta Mayar Wa Gwamnatin Tarayya Rarar Kuɗi Har Biliyan N3.51
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantun Gaba da Sakandare, JAMB, ta ce mayar wa Gwamnatin Tarayya rarar kuɗi har naira biliyan N3.51.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Huɗɗa da Jama’a na JAMB, Fabian Benjamin, ya fitar ranar Laraba.

Mista Benjamin ya ce mayar da wannan rarar kuɗi “yana daga cikin jajircewar Farfesa Is-haq Oloyede wajen ririta dukiyar al’umma”.

Sai dai wani babban jami’in Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU, Laja Odukoya, ya siffanta wannan halayya ta JAMB a matsayin ‘alamar zaluntar al’umma da gwamnatin Najeriya take yi’.

Mista Odukoya, wanda shi ne Shugaban ASUU na Shiyyar Legas ya ce: “Ya zama dole ‘yan Najeriya su kalli hazaƙar da ake cewa hukumar jarrabawar ta yi, kuma su fahimci abin da ake cewa zalunci”.

Sai dai Mista Benjamin ya ƙi cewa uffan a lokacin da aka tuntuɓe shi game da iƙirarin Mista Odukoya.

JAMB ta ce tun a 2016, lokacin da Mista Oloyede ya fara mayar da rarar kuɗi ga gwamnati, wannan al’ada ta ci gaba.

A cewar hukumar, wannan al’ada ta sa kuɗin rijistar jarrabawar hukumar ya ragu daga N5,000 zuwa N3,500.

Ta ƙara da cewa ta ɓangaren ragin da aka samu, an alkinta wa iyaye da wakilansu fiye da biliyan N3 a matsayin kuɗin rijistar jarrabawar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan