Muna tare da Maryam Umar Kofar Mata ɗari bisa ɗari – Matasan Jihar Kano

344

Ƙungiyoyin matasa daban daban a jihar Kano sun bayyana goyon bayansu ga fitacciyar yar siyasar nan da ke jihar, Hajiya Maryam Umar Kofar Mata akan dukkanin wani ra’ayinta a siyasar jihar.

Matasan sun bayyana hakan ne a jiya Talata a lokacin ƙaddamar da wata sabuwar tafiyar siyasa mai taken ‘Ƙafarki – Ƙafarmu Jagora’. Tafiyar siyasar da ke nuna goyon baya ga Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura domin zama gwamnan jihar Kano a shekarar 2023.

Lokacin da ake kaddamar da siyasar ‘Ƙafarki – Ƙafarmu Jagora

Alhaji Arusi Shazali Dala, wanda yana ɗaya daga cikin shugabannin kungiyoyin da su ka yi jawabi ya bayyana cewa irin halaye nagari da kuma ƙoƙarin kyautatawa matasan jihar Kano da Hajiya Maryam ɗin ke yi ne ya sanya su ke ƙara nuna goyon bayansu ga tsarin tafiyar siyasarta.

Hajiya Maryam Umar Kofar Mata

“Hajiya Maryam Umar Kofar Mata ƴar siyasa ce mai halin kirki wacce ta ke taimakon ƴan siyasa na ƙasa musamman mata da matasa. Kuma tana ƙoƙarin ganin matasa sun amfana a dukkanin wata tafiyar siyasa a jihar Kano”

Ya ƙara da cewa “zamu cigaba da bata goyon baya da kuma tallata manufofin dukkanin wani ɗan takara da ta ɗakko”

Shi ma a nasa ɓangaren Abdulfatah A Gambo yabawa kokarin Hajiya Maryam ɗin ya yi akan yadda ta ke kyautatawa matasa a jihar Kano wanda hakan ne zai rabasu da siyasar daba da kuma shaye – shaye.

“Mun gamsu Hajiya Maryam Jagora ce wacce ta ke ƙoƙari domin ganin rayuwar matasa a jihar Kano ta inganta”

Shi kuwa Sadiq Birni misali ya bayar akan yadda Maryam Kofar Matan ke ƙoƙari wajen gina rayuwar matasa ta hanyar ba su jari domin dogaro da kai.

“A makon jiya ta baiwa mata da matasa jari na miliyoyin naira, ta baiwa matasa motoci ta raba musu babura sababbi guda 20, duk da nufin amfana da romon demokradiyya da kuma dogaro da kai”

A nata ɓangaren Hajiya Maryam Umar Kofar Mata godewa matasan ta yi akan irin yadda su ke bata goyon baya tare kuma da bukatar su da su kasance masu bin doka da oda a lokutan da su ke harkokin siyasarsu.

A ƙarshe ta yi kira ga al’ummar jihar Kano da su je su sabunta rijistarsu musamman waɗanda shekarunsu su ka kai tare da buƙatar su adana ta domin da ita za su yi amfani wajen zaɓar Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura a kakar zaɓen shekarar 2023 da ke tafe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan