Pantami Ya Samu Kyautar Minista Mafi Hazaƙa A Afirka Ta Yamma

176

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Intanet na Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu kyautar Minista Mafi Hazaƙa a Afirka ta Yamma daga wani kamfanin hadahadar Intanet mai suna ioSafe Nigeria.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziƙin Intanet ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Laraba.

“Duba da hazaƙarsa a ɓangaren Yaɗa Labarai da Fasahar Sadarwa, ICT, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Intanet, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu kyautar Minista Mafi Hazaƙa a Afirka ta Yamma”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa an ba Minista Pantami kyautar ne a wani taro mai laƙabin 1st Nigeria Data Expo Conference 2021 da aka yi ranar 5 ga Oktoba, 2021.

Amma an gabatar da kyautar ga Minista Pantami ne a hukumance a harabar Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziƙin Intanet, Abuja, ranar Larabar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan