Bankuna da yawa sun garƙame rassansu a Najeriya – Rahoton IMF

262

Wata ƙididdiga da hukumar bayar da Lamuni ta Duniya (IMF) ta fitar da nuna cewa bankunan Najeriya sun garƙame da yawa daga cikin rassansu a ƙasar nan. Wannan lamari ya jawo ƙara jefa al’umma cikin ruɗani da ƙarin wahala a wajen hadahadar kuɗi, musamman a wasu yankunan Najeriya.

Haka kuma rahoton ya ƙara da cewa lamarin ya ƙara jawowa Najeriya cibaya a harkokin hadahadar kuɗi a tsakanin al’umma.

Rahoton na asusun na IMF ya tabbatar da cewa bankuna daban-daban sun rufe rassanau har guda 234 a faɗin ƙasar nan, inda kuma ATM guda 649 suka daina aiki a shekarar 2020. Hakan kuwa ya jawo koma-baya idan aka kwatanta da ƴan shekarun baya.

Ko da a wasu yankuna na Arewacin ƙasar nan akwai bankuna da yawa da suka rufe rassansu, suka daina aiki tun a lokacin annobar Korona, kuma har zuwa yanzu ba su dawo aiki ba.

Wasu daga cikin al’umma dai suna ganin bankunan suna amfani da wannan dama ne domin ƙara gallazawa al’umma da kuma jefa su cikin halin matsatsi a lokacin da suke ƙoƙarin amfani da kuɗaɗen ajiyarsu da ke bankunan.

A yanzu haka dai, galibin jama’a sun koma amfani da na’urar POS domin cirar kuɗi, wanda hakan yake nuna ƙarin cajin da za a ɗibarwa mutum daga cikin lalitarsa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan