Muna Ƙoƙari Wajen Bunƙasa Noman Albasa— Ganduje

383


Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira da a samu ƙanana, matsakaita da manyan-manyan injinan shuka don inganta noman kayan lambu a jihar.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da yake jawabi ga mahalarta Taron Haɓaka Noman Albasa Karo na 4 a Fadar Gwamnatin Kano.

Gwamna Ganduje, wanda Mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, ya wakilta, ya ce kasancewar Kano jiha ta uku a noman albasa, gwamnatinsa tana aiki tuƙuru don haɓaka samar da albasar

“Saboda dagewarmu wajen haɓaka darajar albasa, muna sauƙaƙa wa manoman albasar hanyoyin da za su iya samun kuɗaɗe da za su mayar da su manyan masu samar da albasar kuma masu fitar da ita”, in ji Gwamna Ganduje.

Gwamna Ganduje ya yabi taron, kuma ya bayyana jin daɗinsa ga waɗanda suka shirya shi bisa kawo shi Kano.

Ministan Aikin Gona da Raya Karkara, Dakta Mahmood Abubakar, wanda ya samu wakilcin Abba Gana Yamani, ya ce ba za a iya bayyana amfanin albasa ba a abincin ‘yan Najeriya, yana mai cewa sauƙin noman albasar ne ya sa manoma ke sha’awar nomanta.

“Najeriya tana daga cikin manyan-manyan ƙasashen masu noma albasa a duniya. A 2012 kaɗai, an samar da aƙalla tan 240,000 na koriyar albasa, da kuma tan 1,350 na busasshiyar albasa a Najeriya, in ji ministan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan