Farfesa Isa Ali Pantami ya gina masallaci a makarantar Sakandaren da ya halarta

377

Ministan sadarwa na Najeriya kuma fitaccen malamin addinin Musluncin nan Farfesa Isa Ali Pantami ya gina masallaci a makarantar Sakandaren kimiyya da ke garin Gombe, wato Government Science Secondary School, Gombe, wacce nan ce Sakandaren da malamin ya yi karatunsa.

Tun da farko shafin magoyan Farfesa Isa Ali Pantami ne da ke dandalin Facebook, wato Hon. Dr. Isa Ali Pantami Support Group su ka wallafa hotunan masallacin tare da bayanin inda aka gina shi.

Masallacin an saka masa suna ‘Masjidul Waalidayn’ wato masallacin bin iyaye.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan