Samar da Jami’ar Al-Istiqama Sumaila, zai kawo Sauyi ga Rayuwar ‘yan Nijeriya – Osinbajo

394

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, SAN ya yaba da kafa Jami’ar Al-Istiqama da ke ƙaramar hukumar sumaila, tare da bayyana kafa jami’ar a matsayin wani ga garumin aiki da zai yi matuƙar tasiri ga rayuwar mutane ta hanya mai ma’ana kuma mai kyau.

Farfesa Osinbanji ya bayyana hakanne a faɗar shugaban ƙasa dake Vila a Babban birnin tarayya Abuja, a ranar Laraba, a ya yin da ya karɓi bakwancin wakilan jami’ar mai zaman kanta ta Al-Istiqama, ƙarƙashin jagorancin wanda ya assasa jami’ar kuma tsohon ɗan majalisar tarayyar ƙasar nan sannan tsohon mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin majalisu Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila OFR, Marafan Rano.

Ta cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai ɗauke da kwanan watan 4 ga Nuwamba, 2021 wanda mataimaki na musamman kan yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa Laolu Akande, ya sanyawa a hannu ta nuna cewa mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana damar da Allah ya bawa Kawu Sumaila a matsayin wata damar da zata taimaki ɗin bin Al’ummar ƙasar nan. Ba wai iya ɗaliban dake cikin jami’ar ba harma jama’ar Nijeriya da duniya baki ɗaya.

Da yake magana kan muhimmancin gudanar da jami’a Osinbaji ya shawarci shugabannin jami’ar da su mai da hankali wajen abinda ya shafi harkar kuɗi yana mai cewa kuɗin gudanar da jami’a yana da matuƙar tsada.

Mataimakin shugaban ƙasa tare da wailin jami’ar Al-Istiqama Sumaila

Harwa yau ya kuma shawarci ‘yan ƙasar nan da su ci gaba da girmama junan su tare da gujewa duk wani aiki da zai kawo rabuwar kai a tsakanin al’ummar wannan ƙasa

Tun da fari shi ma a nasa jawabin shugaban jami’ar ta Al-istiqama Hon. Kawu Sumaila, ya bayyana mataimakin Shugaban ƙasa farfesa yemi Osinbanjo a matsayin wani nagar taccen mutum mutum abin koyi wanda al’umma da dama ke son amfana daga cikin baiwar ilimin da Allah ya bashi.

Inda Shi ma a nasa jawabin mataimakin shugaban jami’ar ta Al-Istiqama Sumaila Farfesa Salisu Shehu, cewa ya yi a matsayin jami’ar da aka gina ta kan tafar kin addini suna so su nunawa duniya cewa Allah na da muhimmanci tare da bayyana buƙatar da ke akwai na dawo da koyar da ilimin addini a makarantu.

Ya kuma ƙarƙare jawabin nasa da bayyana Osinbajo a matsayin wani kwararren mai ilimin kuma jagora mai na garta wanda su ke kallo a matsayin shugaba.

Zuwa yanzu dai jami’ar ta Al-Istiqama ta fara da kimanin ɗalibai ɗari biyar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan