Ya kamata gwamnonin Najeriya su yi koyi da Aminu Tambuwal – Alhassan Ado

567

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, kuma a jigo a jam’iyyar APC, Alhassan Ado Doguwa ya yi kira ga gwamnonin ƙasar nan da su yi koyi da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP wajen ayyukan raya ƙasa da cigaban al’umma.

Alhassan Ado Doguwa, wanda shi ne ɗan majalisa mai wakilatar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada da ke jihar Kano, ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a lokacin da ya kai ziyarar duba ayyukan da gwamna Aminu Tambuwal ya ke gudanarwa a jihar ta Sokoto.

Shugaban masu rinjayen wanda ke riƙe da sarautar Sardaunan Rano ya ƙara da cewa bai yi mamakin yadda Gwamna Tambuwal ke yin ayyukan raya ƙasa da cigaban al’ummar jihar Sokoto ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda ya samar da cigaba mai yawa a lokacin da ya ke shugabantar majalisar dokokin Najeriya.

Alhassan Ado Doguwa ya ce tarihin majalisar dokokin Najeriya ba zai taɓa mantawa da Aminu Tambuwal ɗin ba.

A lokacin ziyarar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Dange Shuni, Bodinga da Tureta, Dakta Shehu Balarabe Kakale Shuni da kuma kwamishinan kuɗi na jihar Sokoto Honarabul Abdussamad Dasuki, da kuma hukumar alhazzai ta jiha Alhaji Mukhtar Maigona, sun zagaya da Alhassan Ado ɗin guraren da gwamnatin Tambuwal ɗin ta ke ayyukan raya ƙasa.

Idan za a iya tunawa dai a cikin shekarar 2018 ne gwamnan na Sokoto ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar ta PDP, inda ya zo na biyu bayan Atiku Abubakar.

A ƙarshe tawagar gwamnatin jihar ta Sokoto sun godewa Alhassan Ado Doguwa bisa wannan ziyarar duba ayyuka da ya kawo jihar ta Sokoto.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan