Yau Mal. Ibrahim Shekarau ya ke cika shekaru 66: Wanne abu za ku iya tunawa a lokacin mulkinsa

571

An haifi Malam Ibrahim Shekarau ne a unguwar Kurmawa da ke jihar Kano, a ranar 5 ga watan Nuwambar 1955, kimanin shekaru 66 da su ka gabata. Ya yi karatun Firamare a makarantar Gidan Makama daga shekarar (1961-1967).

Ya yi karantun sakandare a Kano Commercial College daga shekarar (1967-1973) sannan kuma ya garzaya jam’iyyar Ahmadu Bello da ke Zaria daga shekarar (1973-1977) inda ya samu takardar shaidar digiri ta farko.

Bayan da ya kammala karatunsa na jami’a, mallam Ibrahim Shekarau ya yi aikin gwamnati, sannan ya koma dakin karatu inda ya zama malamin lissafi a Government Technical College da ke Wudil a shekarar 1978, bayan shekaru biyu ne kuma ya zama shugaban makarantar Government Day Junior Secondary School a Wudil.

A shekarar 1980 an koma da shi makarantar Government Secondary School da ke Hadejia, sannan Government College Birnin Kudu a 1986, sai kuma Government Secondary School a Gwammaja da kuma makarantar Rumfa College a 1988, duk a matsayin shugaban makaranta.

Daga nana dai mallam Shekarau ya zama mataimakin darakta a harkar illimi a shekarar 1992, bayan kuma shekara guda aka mayar da shi darekta.

Daga nan dai likkafa ta ci gaba inda ya zama babban sakatare a ma’ikatar harkar illimi.

A watan Fabrerun shekarar 2000, malam Shekarau ya koma aikin gwamnati, kafin a koma da shi kwalejin share fagen shiga jam’ia a matsayin babban malamin lissafi.

A nan dai Shekarau ya ajiye aiki da gwamnati bayan ya yi aikin na tsawon watanni 17 a kwalejin.

Siyasa

Ba’a dauki Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wani dan takara da zai yi tasiri ba a zaben gwamnan da aka yi a shekarar 2003 a jihar, amma daga baya kuma sai ya yi tasiri inda ya lashe zaben.

Kuma Malam shekarau ya kafa tarihi inda ya zama gwamna na farko da aka zabe shi a karo na biyu a matsayin gwamna a jihar Kano.

Sardaunan Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya nada shi a matsayin Sardaunan Kano a karon farko a tarihin masauratar Kano.

Malam Ibrahim Shekaru ne dai dan takarar shugaban kasa, karkashin inuwar jam’iyar ANPP a Zaben watan Afrilu na shekarar 2011.

Gudunmawarsa Ga Jihar Kano A Lokacin Da Ya Ke Gwamna

Malam Ibrahim Shekarau, a matsayinsa na wanda ya riƙe jagorancin jihar Kano a matsayin gwamna na tsawo shekaru takwas ya bayar da gagarumar gudunmawa. Fitattu daga cikin irin abubuwan da ya yi akwai:

 • Kafa Hukumar Adaidaita Sahu: Hukumar da ta riƙa tsaftacce tarbiyyar jama’ar jihar Kano. Daga cikin abubuwan ambato da wannan hukuma ta bari akwai samar da babur mai ƙafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep amma a Kano ake kiran sa da Adaidaita Sahu har yau ɗin nan.
 • Ya yi manya da ƙanan titunan da suka riƙa harhaɗa tsakanin karkaru da dama.
 • Kafa Hukumar walwala da jin daɗin alhazai ta Kano (Hajj Commission).
 • Inganta Shari’ar Musulunci.
 • Kafa Hukumar Yaƙi da Rashawa.
 • Kafa Hukumar Hisba.
 • Ciyar da Abicin Kyauta a Lokacin Azumi.
 • Kafa Asibitin Gingiyu da na Titin Gidan Zu.
 • Gina sababbin makarantun firmare da sikandire.
 • Hana karɓar kati a asibiti.
 • Rabawa malaman manyan makaratun (Lecturers) kwamfuta kyauta dan gudanar da nazari.
 • Kafa sabuwar ma’aikatar mata (Ministry of Women Affairs and Social Welfare).
Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan