Kwana Ɗaya Da Ziyarar Ɗanjuma Goje: Ƴarsa ta dangwarar da muƙamin kwamishina

318

Ƴar tsohon Gwamnan jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar jihar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Muhammad Ɗanjuma Goje, wato Dakta Hussaina Ɗanjuma Goje ta ajiye muƙaminta.

Dakta Hussaina Danjuma Goje ta yi murabus daga kujerarta ta Kwamishiniyar Muhalli da Gandun Daji, ta sanar da hakan ne a wani gajeren jawabi da ta yi na Bidiyo ga kafafen yaɗa labarai a yau Asabar a Gombe.

Wannan dai yana zuwa kwana ɗaya da aka samu hatsaniya tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan jihar kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya Sanata Danjuma Goje da na gwamna Inuwa Yahaya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan