Chukwuma Soludo na jami’yyar APGA na kusa da lashe zaɓen jihar Anambara

348

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma ɗan takarar Gwamnan jihar Anambara a tutar jam’iyyar APGA Farfesa Chukuma Soludo na kusa da lashe zaɓen gwwmnan jihar da aka gudanar a jiya Asabar.

Sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta fitar a yanzu ya nuna yadda Chukuma Soludo ya lashe ƙananan hukumomi guda 6 da gagarumar nasarar.

Jihar ta Anambara dai tana da kananan hukumomi guda 21, inda ake ganin jam’iyyar ta APGA ta lashe mafi yawan ƙananan hukumomin.

Ƙananan hukumomin da Soludo ɗin ya lashe sun hada karamar hukumar Orumba ta kudu da Orumba Arewa da kuma Njijoka da Awka ta Kudu da Onitsha ta kudu da Aguata da Anaocha da kuma ƙaramar hukumar Anambra ta gabas.

Haka kuma sakamakon da ya hukumar INEC ta fitar ya nuna cewa har kawo yanzu babu wata ƙaramar hukuma da jam’iyyun APC da PDP su ka lashe.

Hakazalika hukumar zaɓen ta INEC ta ce an samu matsaloli da suka kawo cikas ga harkokin zaɓen gwamnan jihar. Hukumar ta kuma amince da cewa wasu na’urorin tantance masu zaɓe sun samu matsala yayin da ta kasa tura jami’anta a wasu wuraren, kamar yadda shugaban hukumar a Anambra Nkwachukwu Orji ya shaida wa manema labarai.

A yau Lahadi ake sa ran hukumar ta INEC za ta fitar da sakamakon zaɓen gaba ɗaya wanda shi ne zai tabbatar da wanene zai mulki jihar ta Anambara a tsakanin Manyan ƴan takarar guda uku da su ka haɗa da ɗan takarar jam’iyyar APGA da ke mulki a jihar Chukuma Soludo da Andy Uba na jam’iyyar APC da kuma Valentine Ozigbo na jam’iyyar PDP.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan