Fatima Aliyu Barau ta zama Fulanin Ingawa ta farko

673

Mai girma Sarkin Fulanin Dambo hakimin Ingawa da ke jihar Katsina, Alhaji Tukur Suleiman Dambo ya amince da nadin Hajiya Fatima Aliyu Barau a matsayin Fulanin Dambo.

Tun da farko Hajiya Fatima Aliyu Barau ɗin ce ta sanar da nadin sarautar da aka yi mata cikin harshen turanci a shafinta na Facebook inda ta nuna godiyarta ga mai girma Sarkin Fulanin Dambo tare da buƙatar addu’a daga al’umma akan wannan matsayi da ta samu.

Fulanin Dambo, Hajiya Fatima Aliyu Barau

Ina mai farin cikin sanar da al’umma cewa Sarkin Fulanin Dambo Alhaji Tukur Suleiman Dambo ya nadani sarautar Fulanin Dambo, kuma za a yi bikin nadin sarautar nan gaba kaɗan in Allah ya amince. Ina neman addu’ar akan Allah ya taimakeni akan wannan sabon matsayi tare da neman kariya daga dukkanin abin ƙi”.

Fulanin Dambo Hajiya Fatima Aliyu Barau

Hajiya Fatima Aliyu Barau ta kasance mace ta farko da aka taɓa naɗawa Fulanin Dambo a tarihin masarautar Ingawa.

Tuni dai al’umma daga ciki da wajen jihar Katsina ke taya Hajiya Fatima Aliyu Barau murnar samun wannan sarauta ta Fulanin Dambo.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan