Amfani da gidan rediyon Vision FM wajen ketamin haddi ya sanya na rushe ginin da su ke amfani da shi – Mahadi Shehu

685

Sanannen ɗan kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Alhaji Mahadi Shehu ya bayyana dalilan da suka sanya shi ya ɗauki matakin rushe gidan Rediyon Vision FM dake Kaduna da sanyin safiyar yau Litinin.

Da yake jawabi a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna, Mahadi Shehu ya ce ya ɗauki matakin ne saboda ƙarfi da dokar ƙasa ta bashi a matsayin sa na mamallakin ginin gidan Rediyon, kuma ya ba da shi aro ne ga shugaban rukunin gidajen Rediyon na Vision, Malam Umar Faruq Musa tun a cikin Shekarar 2018 ba tare da ya nemi a bashi ko sisin kwabo ba.

Mahadi Shehu

“Umar Faruq Musa ya koma da baya yana cin duddugena ta hanyar amfani da ake yi da gidan Rediyon Vision na Katsina ana cin mutunci na wanda hakan ya saɓa dokar aikin jarida, kuma aka hanani yin magana domin in kare kai na a gidan rediyon” In ji Mahadi Shehu.

Ya ƙara da cewar shugaban rediyon Vision ya cigaba da keta min haddi tare da nuna tamkar babu wata alaƙa dake tsakaninmu, wannan ne ya sanya a matsayi na mai ginin da gidan Rediyon ya ke na rubuta takardar neman gidan Rediyon ya tashi ya bani wurin ta hanyar bada wa’adin shekara guda, amma a wata ziyara da na kai gidan rediyon sai na ga babu wasu kayayyakin da za a yi wahalar cirewa, saboda haka sai na mayar da wa’adin zuwa watanni huɗu.

Haka kuma Mahadi Shehu ya ce bayan da wa’adin ya cika Umar Faruq Musa bai tashi ba, hakan ya sanya shi zuwa ya yaye rufin ginin da cire gate, inda shi kuma Umar Faruq Musa ya kai ƙararsa ga hukumar ƴan sanda yana zargin Mahadi Shehu ya yi mishi kutse cikin gidan Rediyo.

A safiyar yau Litinin ne dai Mahadi Shehu wanda gwamnatin jihar katsina ke shari’a da shi a kotu bisa zargin ɓata mata suna ya jagoranci tawagar wasu matasa da ake zargin ƴan daba ne zuwa gidan rediyon Vision FM Kaduna in da suka rushe ginin gidan tare da ɓata wasu kayayyakin yaɗa labarai.

Wani ɓangare na ginin Vision FM Kaduna da Mahadi Shehu ya jagoranci ruguzawa

Wanda sakamakon hakan dole gidan rediyon ya dakatar da gudanar da aikinsa a Wannan lokacin a jihar Kaduna.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan