Tsohon Sarkin Kano, kuma Halifan Tijjaniyya a Najeriya, Muhammad Sanusi II, zai fara karatun digiri na uku a Jami’ar Landan, Birtaniya.
Tsohon Sarki Sanusi, wanda ya bayyana haka ga editan jaridar Intanet, PREMIUM TIMES ranar Litinin, ya ce kwanan nan ya koma Landan don yin digirin na uku.
A farkon 2019, Sanusi II ya samu kyautar digirin girmamawa a Fannin Kuɗi a wata makaranta mai suna School of Oriental and African Studies, SOAS, Jami’ar Landan.
A 1997 ne Sanusi II ya kammala digirin farko a Nazarin Addinin Musulunci a Jami’ar Ƙasa da Ƙasa ta Afirka, Khartoum, Sudan.
Haka kuma, a 1981, Sanusi II ya yi wani digirin na farko a Tattalin Arziƙi a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Jami’ar Oxford, Landan, ta ba Sanusi II matsayin malamai mai ziyara.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, wanda kwaɗayinsa a ilimi ba zai misaltu ba, a iya cewa yana ɗaya daga cikin ‘yan Najeriya mafiya ilimi da ya taɓa zama Sarki.
A halin yanzu zai haɗa Sanusi II zai riƙa tauna raura biyu ne; kasancewa malami mai ziyara a Jami’ar Oxford, kuma ɗalibi mai karatun digiri na uku a Jami’ar Landan.
Wata biyar bayan an cire shi daga Sarkin Kano, sai Jami’ar Oxford ta amince da buƙatar Sanusi II ta zama malami mai ziyara.