Ɗan Majalisa A Kano Ya Ɗau Nauyin Karatun NCE Na Marayu 20

283

Muhammad Ali, ɗan majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Wudil/Garko, ya ɗauki nauyin karatun wasu marayu mata har su 20 don yin karatun samun Shaidar Malanta ta Ƙasa, wato NCE.

Ɗan majalisar ya bada wannan tallafin ne ta hanyar wata gidauniyarsa mai suna Engineer Ali Wudil Foundation, a cewar Shugaban Gidauniyar, Baffa Wudil.

Yayin da yake jagorantar bikin raba raba tallafin karatun ga watan ranar Litinin, Baffa ya ce dukkaninsu ‘yan ƙaramar hukumar Garko ne.

Ya kuma miƙa wa matan rasiti na biyan kuɗin makarantarsu da kuma wasu kayan karatu don sauƙaƙa musu koyo.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan