Akwai Kyautar Miliyan 5 Ga Duk Wanda Ya Bayyana Maɓoyar Masu Garkuwa Da Mutane A Ekiti— Rundunar ‘Yan Sanda

271


Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Ekiti ta ce za ta bada kyautar naira miliyan N5 ga duk wanda ya bada ingantaccen bayanin inda masu garkuwa da mutane suke ɓoye a jihar.

Sunday Abutu, Jami’in Huɗɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan ne ya bayyana haka ranar Talata a babban birnin jihar, Ado-Ekiti.

Jami’in ya ce sun kama wasu masu garkuwa da mutane da suka haɗa da Banji Akeem, Samuel Ebira, Dele Jimoh da Dayo Igwe.

Mr Abutu ya ce sauran masu garkuwa da aka kama ne suka bayyana sunayen waɗannan mutane huɗu.

Ya ƙara da cewa waɗannan mutane huɗu sun yi garkuwa da shahararrun mutane a Ekiti a shekaru biyu da suka gabata.

A cewar Mista Abotu, waɗannan mutane da aka kama sun amsa cewa sun yi garkuwa da mutane a lokuta daban-daban a jihar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan