Bacci Da Wuri Na Hana Kamuwa Da Ciwon Zuciya— Bincike

385

Wani sabon bincike da aka gudanar a Birtaniya ya gano cewa waɗanda suke kwanciya bacci tsakanin karfe 10:00 zuwa 11:00 na dare sun fi waɗanda ba sa kwanciya da wuri lafiyayyar zuciya, kamar yadda BBC Hausa.

Wasu ƙwararru daga Cibiyar Biobank ne suka gudanar da binciken akan mutane 88,000, inda suka gano mutane masu kwanciya bacci da wuri ba sa cikin haɗarin kamuwa da ciwon bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki.

A halin yanzu dai masan kimiyya sun ce akwai buƙatar ƙara faɗaɗa bincike akan ƙarin mutane domin fahimtar dalilan da suka sanya haɗarin kamuwa da ciwon zuciyar da kuma hanyar magancewa.

Sai dai sun amince cewa yin bacci da wuri da samun isasshen baccin ba tare da wata matsala ba na da muhimmanci ga lafiyar ɗan-Adam

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan