Tsananin tsada ta sanya za a daina shigo da Gas ɗin girki Najeriya

475

Yan kasuwar da ke shigo da Gas din girki Najeriya sun ce za su daina shigo da shi kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa farashin shigo da shi ya karu da kashi 240 akan ko wacce tukunya mai kilo 12.5, wannan na nufin farashin ya karu daga naira 3,000 zuwa naira 10,200 daga tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba 2021.

Kimanin kashi 65 na Gas din da ake girki da shi a Najeriya shigowa da shi ake daga waje, yayin da wanda ake samarwa a cikin gida yakai kashi 35, dakatar da safarar Gas din zai iya kara tsadar Gas din da ake amfani da shi.

Shugaban ‘yan kasuwar da ke shigar da Gas din Najeriya Bassey Essien,ya shaida wa manema labarai cewa kara kudaden futo da kuma kudaden haraji kan Gas din shi ne dalilin da zai sa ‘yan kasuwar su dakatar da shigo da shi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan