Abubuwa 25 Da Ba Ku Sani Ba Game Da Saudiyya

    518

    Abdul-Aziz bin Saud shi ne ya samar da Masarautar Saudiyya. Sarki Abdulaziz, wanda aka haifa a 1902, ya rasu ne a 1947, kuma ya bar ‘ya’ya 34.

    Daga cikin ‘ya’yan 34, 18 suna raye raye a halin yanzu.

    Sarkin Saudiyya na yanzu shi ne Salman bin Abdul-Aziz, Yarima Mai Jiran Gado kuma shi ne Muhammad Bin Salman Bin Abdul-Aziz.

    Mata A Saudiyya

    Ana kiran Saudiyya Al-Mamlakah al-‘Arabiyyah as-Su‘ūdiyyah. Ita ce ƙasa mafi faɗin ƙasa a Yammacin Nahiyar Asiya, kuma ta biyu mafi girma bayan Aljeriya.

    An raba Saudiyya zuwa larduna 13. Su ma lardunan an raba su zuwa gundumar gwamnoni 118.

    Saudiyya ta shiga Majalisar Ɗinkin Duniya, UN, a 1945 kuma ita ce ta samar da ƙungiyoyin Arab League, Gulf Cooperation Council, Muslim World League da kuma Organization of the Islamic Conference, OIC.

    Tana taka muhimmiyar rawa a Asusun Bada Lamuni na Duniya, IMF da Bankin Duniya. Ta shiga Hukumar Kasuwanci ta Duniya, WTO, a 2005.

    A matsayin wadda ta samar da Ƙungiyar Ƙasashen Masu Arziƙin Man Fetur, OPEC, tana kuma ƙoƙarin daidaita kasuwar man fetur ta duniya.

    Taken Saudiyya shi ne: “Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne”.

    Abubuwa 24 Masu Ban Sha’awa Game Da Saudiyya

    1. Ita ce ƙasa ta 14 mafi girma a duniya.
    2. Ita ce ƙasa mafi girman faɗin ƙasa mai sahara.
    3. Tsarin hadahadar bankinta yana ɗaya daga cikin mafi kyau a duniya.
    4. Ba ta karɓar haraji daga ‘yan ƙasar.
    5. Tana kula da lafiyar ‘yan ƙasar kyauta.
    6. Tana bayar da ilimi kyauta.
    7. Duk shekara tana ba ɗaliban da su ke jami’o’in gwamnati dalar Amurka 264, kimanin naira N132,000.
    8. Ƙasa ce mai amfani da tsarin sarauta, saboda haka duk iko yana hannun sarki.
    9. Tana kashe kaso 25 cikin ɗari na kasafin kuɗinta akan ilimi (ƙananan makarantu da jami’o’i.
    10. Ba ta da tafkuna ko koguna.
    11. Bankin Duniya ya ce ita ce ƙasa mafi kyan yin kasuwanci a Gabas ta Tsakiya.
    12. Babban abin da ta ke fitarwa shi ne man fetur, kuma abubuwan da ta fi shigowa da su su ne makamai da ababen hawa.
    13. Kaso 75 cikin ɗari na al’ummar ƙasar matasa ne ‘yan ƙasa da shekara 35.
    14. Tsaka-tsakin shekarun ‘yan ƙasar shi ne 18.
    15. Ana ba mata ma’aikata hutun shekara biyu idan su ka haihu, kuma ana biyan su a duk tsawon wannan lokaci.
    16. Tana da idaniyar ruwa mafi girma a duniya wadda ta ke a Jidda, a kan Tekun Maliya.
    17. Tana da filin jirgin sama mafi girma a duniya, Filin Jirgin Saman Sarki Khaled, Riyad.
    18. Tana da matatar ruwa mafi girma a duniya, wadda ta ke a Jubail.
    19. Ita ce ƙasa ɗaya da ta haramta wa mata tuƙi a duniya. Amma a shekarar 2019 ta janye haramcin.
    20. Gininta mafi tsawo shi gini ne na 31 mafi tsawo a duniya, wato The Kingdom Center a Riyad.
    21. Kaso 21 na al’ummar ƙasar ‘yan ƙasashen waje ne.
    22. Birninta mafi girma, Riyad, yana da yawan jama’a da ya kai 4,193,000, kuma na 69 a girma a duniya.
    23. A halin yanzu ana siyar da galan ɗin ɗaya na gas a ƙasar kan farashin santi 60.
    24. Kasuwarta ta hannu jari, Tadawul, ita ce kasuwar hannun jari ta 11 mafi girma a duniya.
    25. Game da yanke hannu, a shekara 10 da ta gabata, mutane 11 kawai aka yanke wa hannu.
    Turawa Abokai

    RUBUTA AMSA

    Rubuta ra'ayinka
    Rubuta Sunanka a nan