Auren Malala Yousafzai ya bar baya da ƙura a Kano

619

Wata matashiya mai rajin kare hakkin mata a kafafen sadarwa na zamani ƴar asalin jihar Kano, Zainab Naseer Ahmad, ta yi barazanar gurfanar da wani matashi mai suna Ibrahim Sarki Abdullahi a gaban kuliya sakamakon zolayarta da ya yi a shafin Facebook akan auren Malala Yousafzai.

Tun da farko Ibrahim Sarki Abdullahi ne ya wallafa hoton Zainab Naseer a shafinsa na facebook tare da wani gajeren rubutu mai taken ‘Malala ta Shushemu’, sai dai daga baya shafin jaridar Labarai24 ya fahimci matashin ya goge wallafar da ya yi.

Wallafar da Ibrahim Sarki Abdullahi ya yi akan Zainab Naseer Ahmad

Jim kaɗan da wallafar ne Zainab Naseer ɗin ta yi wani rubutu cikin harshen turanci. Ga dai fassarar abin da Zainab ɗin ta rubuta “Ina amfani da wannan rubutun ne domin in sanar da Ibrahim Sarki Abdullahi cewa ina kan shirin ɗaukar matakin shari’a a kansa tare da neman diyyar batamin suna da ya yi ta hanyar amfani da saka hotona a bainar jama’a. Na tuntubi ‘yan uwana da abokan arziki akan wannan al’amari kuma na yarda da shawarwarin da suka ba ni na ɗaukar mataki bisa doka don kare kaina da kiyaye mutuncina”.

Sakon Zainab Naseer Ahmad ga Ibrahim Sarki Abdullahi

Zainab Naseer Ahmad ta yi fice a kafafen sadarwa na zamani, la’akari da yadda ta ke furta ra’ayinta ba tare da fargaba ko shakka ba, duk da cewa maganganunta na janyo mata ce-ce-ku-ce.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan