Da gaske Sheikh Ibrahim Zakzaky zai fito takarar shugabancin Najeriya?

451

Ƴan Harka Islamiyya (IMN) sun ƙaryata labarin da ke yawo cewa Malamin su yana shirin fitowa takarar shugabancin kasar Najeriya.

Hakan yazo cikin wata sanarwar manema labarai da mataimakin shugaban dandalin yada labarai na Harkar Musulunci, Abdullahi Usman ya fitar a jiya Laraba 10/11/2021.

”Hankalin mu ya karkata ne a kan wani hoton da ke alakanta Shaikh Zakzaky da muradin tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Wannan aiki ne da wasu miyagu ke yi don cimma mummunar manufarsu.” in ji shi

Ya cigaba da cewa ”Kasancewar Shaikh Zakzaky babban malamin addinin Musulunci ne kuma Sen. Kwankwaso sanannen ɗan siyasa ya isa a kansa ya nuna wautar masu wannan shiri na rashin hankali.”

Sheikh Ibrahim Zakzaky

Abdullahi ya kuma ce Zakzaky ba zai taba tsayawa takara a kowane matsayi na siyasa a Najeriya ba duk da cewa a matsayinsa na dan Najeriya yana da ‘yancin yin haka, amma a matsayinsa na Malamin Musulunci ba zai taba shiga wata jam’iyyar siyasa ba.

A ƙarshe ya yi kira ga al’umma da su yi watsi da waccan Fasta da ake yaɗawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan