Kotu Ta Hana ‘Yan Sanda Kama Nasir Salisu Zango

468

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abdu Maiwada Abubakar ta hana Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Ismaila Dikko, da wani ɗan sanda mai suna Inspector Friday kama fitaccen ɗan jaridar nan, Nasir Salisu Zango.

A ranar Alhamis ɗin ne kotun ta yi wannan hani, bayan ta saurari lauyan mai ƙara, Abba Hikima.

A yayin gabatar da shirin In Da Ranka na Freedom Radio, Kano, Nasiru ya kawo wani rahoton yadda wasu jami’an ‘yan sanda su ke karɓar maƙudan kuɗaɗe daga wurin jama’a da sunan beli.

Sakamakon rashin gamsuwa da rahoton ne sai Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano ya bada umarnin kama Nasir.

Bayan Nasir ya ji labarin kamun ne sai ya garzaya kotu don neman ta hana a kama shi.

Kotun ta ɗaga ƙarar zuwa 19 ga Nuwamba, 2021 don ci gaba da sauraro.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan