Gumulawa da alƙawarin mai ‘Kalkuleta’

    357

    Ɗazu da na ke karanta wai Gwamna Badaru Abubakar ya ce zai gina asibitin ƙashi a Gumel hanyar Gagarawa, ban san lokacin da dariya ta ƙwace min ba. Wato mu ma tsiyar kalkuleta ta zo kanmu kenan!

    To ka da a ce ina yi wa garinmu buƙulu don za a gina mana gidan ɗori, amma dai na san wannan zance ne kawai wanda kuma ba ya rasa nasaba da al’amarin 2023. Don haka, ka da ma ku ɗauka ku rataya.

    In ban da dai an ɗauki mutanen Jigawa masu ƙwaƙwalwar ‘Sweet Campo’, daga cikin ɗimbin asibitocin da gwamna ya riƙa yawo gari-gari yana yin alƙawarin ginawa a faɗin jihar, nawa aka kammala aikinsu zuwa yanzu? Shin ina labarin sabon babban asibitin Haɗeja ne? To wanda ya kasa gina general hospital ɗaya a cikin sama da shekaru biyar shi ne ku ke tsammanin zai gina muku orthopaedic a ɗan lokacin da ya rage masa akan mulki?

    Gwamna Muhammad Badaru Abubakar da mai martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani

    A ɗauka ma da gaske yake saboda yana neman ƙuri’unku a takarar sanata a 2023. Shin asibitin ƙashi shine babban abin da ‘yan yankin masarautar Gumel suka fi buƙata a halin yanzu? Yara nawa ne suke ta gararamba da kwalin NCE a yankin babu aikin yi, alhalin ga makarantu nan babu malamai ko kayan aiki? Kuma da wanne kuɗi za a yi wannan asibitin, musamman a yanzu da gwamnatoci suke kukan rashin kuɗaɗe da matse bakin aljihu, sannan kuma, uwa uba, shekarar zaɓe tana gabatowa?

    Na san ko an fara wannan gini, babu inda zai je za a watsar da shi; kawai za a yi amfani da shi ne domin kamfen a 2023, a wanki garori su bada ƙuri’unsu, asibiti kuwa sai dai a gwamnati ta gaba in da rabo. Ko ba komai dai, shi ai ya tsira da jami’ar gwamnatin tarayya a shiyyarsa, wadda za a iya cewa ta fi zama tabbas akan asibitin ɗorin karaya da za a yi mana wala-wala da shi.

    Ni da na ji an ce a hanyar Gagarawa za a gina asibitin ƙashin, har na fara tunanin ko a gonakin talakawa da suka ƙwace da sunan noman rake za a yi, tun da yanzu an ce sun fasa noman raken. (Dama mun san akwai lauje cikin naɗi!). Aƙalla a riƙa kai mutanen da motocin kamfani suke rafkewa a hanyar.

    Don haka, ban ce ka da ku yi murna ba, amma dai wannan aiki tarkon 2023 ne. Babu mamaki idan gobe ku ka ji ya ce zai gina asibitin warkar da matasa masu shan kayan maye a Kazaure.

    Hamisu Gumel ya rubuto daga Abuja

    Turawa Abokai

    RUBUTA AMSA

    Rubuta ra'ayinka
    Rubuta Sunanka a nan