Cibiyar ƴan jaridu da fasahar sadarwa ta Afrika wato Africa Media and Information Technology Initiative (AfriMITI) ta shiryawa ƴan jaridu da ƙungiyoyin fararen hula daban daban taron ƙarawa juna sani kan buƙatar da ke kwai na samawa kai tsaro a yayin amfani da shafukan intanet.
Taron wanda ya mai da hankali wajen nunawa mahalarta yadda ta kamata su dinga yi wajen ɓoye sirrikansu a wannan ƙasa da kuma samar da hanyoyin kariya ga ƴan ƙasar da kuma bayyana hanyoyin cigaba wanda cibiyar ƴan jaridu da fasahar sadarwa ta Afrika wato Africa Media and Information Technology Initiative (AfriMITI).

Tun da farko a nasa jawabin babban daraktan cibiyar Malam Garzali Haruna Ibrahim, cewa ya yi a matsayin su na mambobin a gamayyar ƙungiyar masu adana bayanai ta duniya sun gudanar da wannan bitar ne domin fito da dabarun haɓɓaka amfani da fa’idar ɓoye bayanan al’umma musamman masu amfani da shafukan intanet.

Ya ƙara da cewa “Mun zaɓi ƴan jarida daga kafafen yada labarai daban-daban domin mu fara koyar da su dabarun yadda za su dinga amfani da fasahar addana bayanai ta hanyar amfani da lambobin sirri, la’akari da irin yadda suke taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan su da su ka haɗa da samar da bayanan sirri wanda ya ƙunshi abubuwa da dama”
“Haka kuma ƴan jaridu na fuskantar ƙalubale da dama ciki harda tsoratarwa da kuma samun tangarɗa a irin kayayyakin da su ke amfani da shi”.

“Kamar yadda al’umma ke bayar da bayanan sirri, za a iya samun wanda zai yi kutse tare da sace bayanan da aka adana su tare kuma da kwarmata su a inda zai zama guri ne haɗari”.
A nasa ɓangaren, wani ƙwararre a harkar kariya a shafukan yanar gizo Engr. M. A Sulaiman, shawartar mahalarta taron ya yi da su dinga yin duba na tsanaki a lokutan da su ke adana bayanan da za su yi amfani da su da kuma manhajojin da ke kan wayoyinsu sadarwa.

Engr. M. A ya ce wasu manhajojin ba na gaskiya ba ne za kuma su iya zama wakilan da za su yi amfani da kai wajen cimma na su buƙatu.
A ƙarshe masanin ya ƙarƙare da cewa ” Irin waɗannan manhajoji su na nan a shafukan intanet don haka ya kamata jama’a su dinga kula wajen amfani da su ta kyakkyawar hanya domin gujewa faɗawa cikin hatsari”