Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, IPMAN, ta tabbatar da cewa akwai isasshen kananzir a Najeriya.
Jami’in Huɗɗa da Jama’a, PRO, na IPMAN, Yakubu Suleiman, shi ne ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa ta waya da manema labarai ranar Asabar.
Yakubu ya ce akwai man fetur da gas a dukkan faɗin Najeriya, ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa da su kwantar da hankalinsu.
“Kada ku tada hankali, akwai isasshen mai a ƙasa da zai isa har shekara mai zuwa”, in ji shi.
Ya yaba wa Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari bisa cire tallafin man fetur da na gas.
Wani wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, da ya zagaya wasu gidajen mai a Babban Birnin Tarayya, FCT, Abuja, ya gano cewa akwai kananzir, amma ana siyar da shi akan N350 duk lita.
NAN ya rawaito cewa ‘yan bumburutu suna siyar da kananzir ɗin tsakanin N420 zuwa N450.