Farfesa Hafsat Ganduje ta yi zarra a tsakankanin matan gwamnonin Najeriya

219

Hukumar gudanarwar COA Media Group da ke birnin tarayya Abuja sun karrama mai ɗakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da lambar yabo ta matar gwamna mafi ƙwazo a cikin matan gwamnonin Najeriya a shekarar 2021.

A lokacin karramawar COA Media Group sun bayyana cewa sun karrama Farfesa Hafsat Ganduje ne da wannan lambar girmamawa ne saboda ƙoƙarin ta na hidima ga al’umma da kuma kawo cigaba a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Lambar yabon da aka baiwa Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje

A nata ɓangaren Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, wacce ta samu wakilcin shugabar mata ta jam’iyyar APC reshen jihar Kano, godewa waɗanda su ka zaɓota tare da bata wannan lambar yabo da kuma alkawarin cigaba da ayyukan alkhairi.

Haka kuma tsohon dogarin shugaban Naijeriya marigayi janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al – Mustapha mai ritaya ne ya mikawa Farfesa Hafsat din lambar yabon.

A ƙarshen taron an ƙaddamar da wata mujalla mai suna Eminence Magazine wacce za ta dinga fita lokacin-lokaci inda a wannan karon ta ƙunshi ayyukan kyautata rayuwar matan jihar Kano da Farfesa Hafsat Ganduje ta ke yi wanda suka hada da bayar da tallafi da kuma koyor da sana’o’i daban-daban da harkar lafiyar mata da kuma ƙananan yara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan