Shugaban Riƙo na Jam’iyar APC a Jihar Zamfara, ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari, Lawal Liman, Shugaban Riƙo na Jam’iyar APC a Jihar Zamfara, ya yi kira ga mabiya tsagin nasu cewa kada su shiga zaɓen shugabannin jam’iya na mazaɓu wanda ɓangaren gwamna mai ci, Bello Matawalle ya gudanar a ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba.
Wannan kiran na ƙunshe ne a wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na ɓangaren, Ibrahim Birnin-Magaji ya fitar a yau Asabar a Gusau.
“Kun san cewa akwai umarnin da kotu ta bayar na a dakatar da duk wani zaɓen shugabannin jam’iya har sai abinda kotun ta yanke a bisa rushe shugabannin jam’iya na jiha daga uwar jam’iyar APC ta ƙasa.

“A kan hakane, jagoran mu, Alhaji Abdul’aziz Yari ya umar ƴan jam’iyar APC a jihar nan, a ƙarƙashin shugabancin Lawal Liman da mu ƙauracewa zaɓukan shugabannin jam’iya tun daga na mazaɓa, ƙanan hukumomi da na jiha wanda gwamna Bello Matawalle ya shirya a yau Asabar, 13b ga watan Nuwamba.
“Sabo da haka ina kira da mu ƙara haƙuri mu kuma zama masu bin doka, sannan mu jira umarnin da za a bayar nan gaba,” in ji shi.