Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai wata ziyara ta musamman jami’ar Swarrnim Startup and Innovation, da ke jihar Gujarat a ƙasar India.

Jami’ar ta Swarrnim Startup and Innovation ta gayyaci Rabi’u Kwankwaso ne a matsayinsa na wanda ya baiwa ɓangaren ilimi gudummawa ta musamman a lokacin da ya mulkin jihar Kano da kuma yanzu.

Jihar Gujarat dai ita ce mahaifar Mahatma Gandhi, mutumin da ake yiwa kallon uba ga daukacin ƴan ƙasar India.
Haka kuma Mahatama Ghandi ya jagoranci fafutuka ta lumana domin kwato Indiya daga mulkin mallakar Burtaniya, inda ya zama gwarzo ga dumbin mutane a fadin duniya.
Turawa Abokai