Sarkin Noman Kano ya tsallake rijiya da baya daga masu garkuwa da mutane

861

Ɗaruruwan mutane a garin Chiromawa da ke yankin ƙaramar hukumar Garun Malam da ke jihar Kano ne su ka tarwatsa wasu masu da ake zargin masu garkuwa da mutane da su yi kokarin yin garkuwa da Sarkin Noman Kano Alhaji Yusuf Nadabo.

Alhaji Yusuf Nadabo mai kimanin shekaru 80 wanda kuma shi ne mamallakin gidan man fetur na Chiromawa, shi ke riƙe da sarautar Sarkin Noman Kano.


Tun da farko jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa da misalin karfe bakwai da rabi da minti biyar na ranar juma’a ne masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai su ka yi wa ofishin na Sarkin Noma da ke bakin Tasha ƙawanya inda su ka dinga harbe – harbe.

Sarkin Noman Kano Alhaji Yusuf Nadabo

Wata majiya ta shaidawa cewa ɗaya daga cikin mazauna garin na Chiromawa ya samu raunuka daga harbin bindigar da masu garkuwar su ka yi a lokacin da su ke ƙoƙarin tarwatsa su.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda ya ce sai dai harin bai yi nasara ba sakamakon ganganko da mutanen gari da ƴan banga su ka yi wa ƴan bindigar.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan