Tsohon ɗan majalisa mai wakiltar Sumaila da Takai a majalisar tarayya Nijeriya kuma hadimin Shugaban Ƙasa kan harkokin majalisa, Abdurrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewa zamanin ƙaƙaba ‘yan takara a siyasar Nijeriya ya wuce.
Kawu Sumaila ya kuma bayyana cewa ya kamata jam’iya mai mulki, APC ta ɗauki darasi a kan zaɓen gwamna na Anambra, inda ɗan takarar jam’iyar APGA, Charles Soludo ya lashe zaɓen.
Kawu Sumaila ya yi wannan kira ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da harshen turanci inda Labarai24 ta fassara a yau Asabar.

A saƙon da ya wallafa, tsohon wakilin Takai da Sumaila a majalisar wakilai ta tarayya ya ce shi bai damu da zaɓen fidda gwani na ‘yar tinƙe ko akasin hakan a APC.
“Ni ban damu da zaɓen fidda gwani na ‘yar tinƙe ko akasin hakan a APC ba, amma dai, ya kamata mu faɗawa kan mu gaskiya zamanin ƙaƙaba ‘yan takara ya wuce. Zaɓen Anambra dai ya kamata ya zame mana izina,” in ji Kawu Sumaila