Fitila: Manyan Rahotanni Da Sharhinsu Na Makon Jiya – Ali Sabo

321

Kamar yadda muka fara labarta muku a makon da ya gabata dangane da taron da ake gabatarwa a birin Glasgow na kasar Scotland wanda kasashen duniya fiye da dari da hamsin suka halarta kan makomar yanayi a duniya, a yanzu ana dab da karkare wannan taro wanda ya dauki tsawon kwanaki goma ana gabatarwa.

Makon da ya gabata mun kawo muku yadda shugabannin manyan kasashen duniya kamar Amurka da Birtiniya harma da yarima mai jiran gado na Birtaniya suka gabatar da jawabai a wurin wannan taro da kuma irin kiraye-kiraye da suka yi kan a hada karfi wurin tunkarar matsalar da sauyin yanayi yake kawowa da kuma barazanar da yake ga rayuwar al’umma.

A wannan mako, zamu yi duba kan jawabin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a wurin wannan taro tare da kuma matsayar da aka cimma zuwa yanzu a taron. A cewar mai bawa shugaban kasa shawara akan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu sakon shugaba Muhammadu Buhari a wurin taron yayi kama dana ‘yan gwagwarmaya.

Shugaba Muhammadu Buhari a tsakiya

Shugaban a farkon jawabinsa ya sanar da mahalatta taron musamman manyan kasashe masu karfin tattalin ariziki cewa Najeriya kamar sauran kasashe masu tasowa ta halicci taron ne kuma a shirye take wurin bayar da ta ta gudunmawar wurin samar da yanayi mai kyau a duniya. Ya kara da cewa lokaci yayi da shugabannin wadannan kasashe ya kamata su fara aiwatar da alkawarurrukan da suka daukarwa duniya.

Shugaban yace duk da dai nahiyar ta Afrika dan abu da take samarwa na dumamar yanayi bai wuce kaso biyar ba amma hakan bai hana shugabannin nahiyar su zo taron ba kuma su bayar da tasu gudunmawar, ya akara da cewa abun takaici ne ace kasashe irin su Sin (China) wacce take samar da kason da ya kai 11 cikin dari na dumamar yanayi da Rasha ba su halarci taron da kansu ba.

In zamu iya tunawa dai ko a makon daya gabata wannan shafi ya kawo muku yadda shugaba Biden na Amurka ya caccaki wadannan shugabanni kan rashin halattarsu wannan taro. Shugaban ya kara da cewa, kasashe da suka sanya hannu akan yarjajjeniyar da akayi a kasar Faransa ya kamata su cika alkawarurrukan da suka dauka musamman wajen tallafawa kasashe masu karamin karfi da kudade wadanda su ne zasu sa a cimma wannan buri.

A karshe shugaban ya ce duk da muhimmancin wannan batu da aka dauko bai kamata ayi gaggawa ba, kamata yayi abi abun a hankali domin kar aje a sami wata matsalar ta daban.

Jawabanin na shugaba Buhari tabbas ya tayar da kura kuma kamar yadda mai bawa shugaban shawara akan harkokin yada labarai malam Garba Shehu ya fada maganar ta shugaban kasan tayi kamata da ta yan gwagwarmaya musamman masu aiki akan dumamar yanayi.

Sai dai wasu na iya cewa shi kansa shugaban in akayi duba da abubuwan da su ke faruwa a kasa Najeriya to bai kamata yayi jawabi a wurin taron bama. Masu wannan batu suna duba da yadda farashin makashin gas na girki kullum ke tashin gwauran zabo a kasar wanda hakan ya sanya al’ummar kasar da dama suka hakura da amfani da shi suka koma amfani da gawayi ko kuma ita ce wanda hakan ke nuni da cewa ana samun ci baya a wannan tafiya.

Sannan Masana na ganin cewa jawabin na shugaba Buhari ya yafi kama da irin jawaban da ko da yaushe shugabannin kasashe masu tasowa su ke yi na neman taimako daga kasashe masu karfin tattalin arziki domin gudanar da wasu aiyuka a kasashensu amma ko da anyi sa’a kudaden sun fito a mafi yawan lokuta sai a tarar abinda aka ce za’ayi da kudaden basu akayi ba. Masana suka kara da cewa watakila rashin bawa kasashen kudi domin gudanar da wannan aiki baya rasa nasaba da wannan zarge-zarge da ake yiwa shugabannin.

Koma dai menene zamu ci gaba da bibiyar wannan batu domin muga matakan da za’a dauka bayan wannan taro.

Bari mu yi duba da harkar tsaro wacce taki ci taki cinyewa a wannnan kasa. A ranar asabar din da ta gabata ne aka samu labarin mayakan Boko Haram sun hallaka babban jami’in soja mai mukamin Brigadier General, wato Brigadier General Dzarma Zirkushu tare da sojojin a lokacin da suke kai dauki ga yan uwansu a garin Bugulwa dake jihar Borno.

Kafin rasuwar mamacin shi ne yake jagorantar rudunar sojoji ta 28 da ke garin Chibok. A cewar kakakin sojoji na jihar Borno yace rudunar tasu sun samu nasarar tarwatsa yan ta’addan tare da kashewa da jikkata da yawa daga cikinsu.

Wannan labari dai abun takaici ni ga kasa Najeriya da kuma iyalin wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan aran gama da akayi da yan ta’addan. Sai dai ko da yaushe kiran da al’umma musamman masana harkokin tsaro shi ne indai ana so ayi maganin wadannan yan ta’adda to dole sai an samarwa da sojoji kayan aiki na zamani domin tun karar wadannan yan ta’adda.

Amma abun takaici sau da dama rahotanni na nuni da cewa ana tura wadannan sojoji ne filin yaki ba tare da ishasshun kayan aiki ba, sannan hakkunansu wadanda ya kamata a rinka basu su ma ba sa samuwa wanda masana na gani yana rage musu kwarin gwiwa.

Sojoji suna sinturi

Haka zalika akwai maganganu da su ke fitowa cewa hatta wadanda suka rasa rayukansu a fagen yaki ba’a biyan iyalinsu hakkunansu ko kuma suna shan wahala kafin hakkokin nasu su fito.

Kiran mu ga gwamnati a nan shi ne ya kamata a tashi tsaye a samarwa da jami’an tsaro kayayyaki na zamani sannan a rinka kula da hakkokinsu.

Batu na gaba da zamu tattauna akai a wanna mako shi ne kan hukumar da ke samar da wutar lantarki ta kasa ta sanar da karin kudin mita da al’umma suke anfani da ita a gidajensu. Sanarwar ta kara da cewa karin zai fara aiki daga ranar 15 ga wannan watan da muke ciki.

Game da wanna batu dai tuni al’umma suka fara guna-guni duba da halin matsi da kunci da al’umma su ke ciki sannan aka fito da wannan batu?

Masu sharhi da masana a wannan bangaren tsumi da tanadi na ganin cewa wannan karin kudade da ake samu a bangaren wutar lantarki zai kawo koma baya game da kudurin gwamnatin tarayya na mai da al’ummar kasa baki daya amfani da mita ta kati duba da yadda farashin nata ke tashi kullum.

Kuna iya bibiyarmu ta kafafen sada zumuntarmu a

Facebook
YouTube
Instagram
Telegram
Ko kuma ku aiko mana da gyara ko shawara ta adireshinmu na email – Labarai24@yahoo.com

Ku shiga group dinmu don samun labaru kullum 👉 WhatsApp

Ali Sabo Dan Jarida Mai Sharhi Akan Al’amuran Yau Da Kullum. Za a iya samunsa ta aliyuncee@gmail.com

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan