Janar Sani ya yaba da ƙoƙarin mutanen Kano bisa daƙile harin masu garkuwa da mutane

185

An yabawa mutanen Kano da musamman al’ummar garin Chiromawa da ke yankin ƙaramar hukumar Garun Malam dangane da ƙoƙarinsu wajen daƙile harin da masu garkuwa da mutane su kai yankin a makon jiya.

Shugaban gidauniyar HISANEF Manjo Janar Ibrahim Sani ne yayi yabon kuma yayi kira ga jama’a da su lura da duk wani abu da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya.

Yayin da yake bayar da tallafi domin gyaran wata rijiyar burtsatse da ke unguwar Yakasai a yankin ƙaramar hukumar Birnin Kano da Kewaye ya bukaci hadin kai don taimako a matakin unguwanni tare da jaddada muhimmancin samun ruwa don magance cututtuka a cikin al’umma.

Haka kuma ja hankalinsu da su taimakawa jami’an tsaro da rahoto tare da sa ido sosai a inda suke.

Shugaban gidauniyar HISANEF Manjo Janar Ibrahim Sani

Janar Sani ya yi kira ga direbobi a jihar Kano da kasa baki daya da su zama masu kyautata aikinsu musamman lokacin yanzu da shekara ke karewa.Ya hore su da su guji kwayoyi da gudu ba bisa ka’ida ba a kan tituna wanda ke jawo asarar rayuka da dukiya.

A cewar sa direbobin kan manyan tituna ya zama wajibi su saka tayoyi masu kyau kuma su saka ruwan burki nagartacce don gudun jefa rayuwar fasinjoji cikin hatsari a watannin karshen shekara.

A ƙarshe Janar Sani ya yaba da ƙoƙarin hukumar kiyaye haddura ta kasa a kokarin ta na kare jama’a ya kuma yi kira da direbobi da masu aikin tashoshin sufuri da su dena loda kaya fiye da ka’ida don kare afkuwar haddura a wannan lokutan hutu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan