Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta cafke wasu masu safarar hodar ibilis mai nauyin kilogram 17 da darajarta ta zarce naira biliyan 4.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Huɗɗa da Jama’a, PRO na NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi a Legas.
NDLEA ta ce ta samu wannan nasara ne lokacin da ta kai samame a wasu sassan Jihar Legas bayan ta samu wasu bayanan sirri.
A cewar hukumar, ta kuma cafke wasu mutane goma da ta ke zargi da safarar miyagun ƙwayoyi
Mista Babafemi ya ce NDLEA ta yi kamen ne a Babbar Tashar Jiragen Ruwa, Apapa da kuma Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammad, Legas.
“Ana bincike kan wasu mutane huɗu yanzu haka a kan hodar ibilis mai nauyin kilogram 13.65 da aka ƙwace a cikin wani jirgin ruwa da ake kira MV Karteria da ya shigo Tashar Jirgin Ruwa, Apapa, daga birnin Santos na ƙasar Brazil a ranar 7 ‘ Nuwamba, bayan makoni uku da cafke hodar ibilis mai nauyin kilogram 32.9 da aka gano a cikin wani jirgin ruwa da shi ma ya fito daga birnin Santos na Brazil.
“An cafke wasu mutane biyar a sassa daban- daban na Legas da Delta waɗanda ake zargin suna da hannu a safarar hodar ibilis mai nauyin kilogram 3.200 da aka samu a hannun wani fasinja da ya shigo cikin ƙasar ranar 5 ga Nuwamba”, in ji shi.