Ta’aziyya: Rasuwar Sani Dangote babban giɓi ne ga harkokin kasuwanci a Afrika – Muhuyi Magaji Rimin Gado

167

Tsohon shugaban Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Malam Muhuyi Magaji Rimin ya bayyana rasuwar Alhaji Sani Dangote a matsayin babban giɓi a bangaren harkokin kasuwanci a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.

Malam Muhuyi Magaji ya bayyana hakan a cikin wani sakon ta’aziyya da aikewa hamshaƙin attajirin nan na nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote a yau Litinin.

A cikin sakon ta’aziyyar Malam Muhuyi Magaji ya bayyana kaduwarsa da jin labarin rasuwar ga labarin Alhaji Sani Dangoten.

Na yi matuƙar kaduwa da jin labarin rasuwar ɗan uwanka Alhaji Sani Dangote, wanda ya rasu a wani asibiti da ke ƙasar Amurka. Tabbas a matsayinsa na mataimakin shugaban rukunin kamfanin Dangote, rasuwarsa babban giɓi ne ga Najeriya da ma nahiyar Afirka

Marigayi Alhaji Sani Dangote

Haka kuma tsohon shugaban hukumar ya ƙara da cewa rashin na Alhaji Sani Dangote wani babban giɓi ne da zai yi wahalar cikewa, la’akari da yadda ya samar da dubban ayyukan yi ga matasan ƙasar nan a lokacin da ya ke riƙe da muƙamin shugabacin mataimakin shugaban rukunin kamfanin Dangote, wanda hakan ya taimaka ƙwarai da gaske wajen rage matsalar rashin aikin yi a faɗin Najeriya.

Haka kuma Malam Muhuyi Magaji ya yi addu’ar neman rahamar ubangiji ga mamacin tare da baiwa iyalansa hakurin wannan babban rashi da aka yi.

A jiya ne dai Allah ya yiwa mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote kuma dan uwa ga hamshakin mai kudin nan Aliko Dangote ya rasuwa a wani asibiti da ke ƙasar Amurka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan