Ana zargin ƙasar Iran da yin amfani da Namiji a matsayin mace a ƙwallon mata

632

Ƙasar Jordan ta zargin kasar Iran da sanya Namiji a matsayin gola a gasar kwallon kafa ta mata da aka buga tsakaninsu. Golan wanda aka ce macece ce ya kade kwallo biyu a cikin hudun da aka buga masa.

Sai dai bayan tashi daga wasan kasar Jordan ta nuna rashin gamsuwa da wasan, inda ta bayyana cewar Golan Iran namiji ne ba mace ba. Tuni dai suka aike da takardar koke zuwa ga hukumar kula da kwallon mata ta Asia cup da ake bugawa yanzu haka.

Golan da aka bayyana sunansa da Zohreh Koudaei, mai shekaru 32. Kasar ta Jordan ta bukaci ayi masa binciken kwakwaf dan gabo cewar mace ce ko Namiji.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan