Hukumar Hisbah a jihar Kano, ta bayyana kudirin cigaba da kai sumame a kai a kai dukkan wuraren da a ke zargin samari da ƴan mata kan hadu, domin aikata badala.
Babban Dataktan hukumar, Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya shi ne, ya furta kudirin a ranar Litinin a shalkwatar hukumar da ke unguwar Sharada a birnin Kano.
Wannan ya biyo bayan wani sumame da dakarun hukumar su ka kai a wurin shakatawa na (NITEL training centre) da ke kan titin Katsina kusa da Hajji camp.
Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya ya cigaba da cewa duba da yadda dakarun hukumar ke cigaba da artabu da irin wadannan samari da ƴan mata a gurare daban – daban a sassan ƙwaryar birnin Kano.

Ya kara da cewa ko da iyaye sun saki yayan su sa – sakai to hukumar ba zata bari ba, kuma za’a cigaba da ɗaukan matakan babu sani – babu sabo.
Dr. Aliyu Musa ya ce burin hukumar bai wuce ganin al’umma a jihar Kano sun zama nagari ba, masu yin biyayya ga dokokin Allah madaukakin sarki.
Hakazalika Dr. Aliyu ya yi addu’ar Allah ya shiryar da matasan jihar maza da matandomin daga cikin su za’a sami shugabani a nan ga ba.
A lokacin sumamen, hukumar Hisbah sun samin nasarar kamo yan mata 11 da saurayin da ya hada bikin zaben sarauniyar kyau, a filin shakatawa na NITEL training centre, ciki har da kwalaben nau’ikan barasa har guda 324, kimanin katon 40.