Kotun shari’ar Muslunci a Kano ta zartar da hukuncin bulala 15 ga ƴan shaye – shaye su 20

303

Kotun Shari’ar Muslunci mai lamba 1, da ke Ƙofar Kudu a cikin Jihar Kano ta yankewa wasu samari 15 hukuncin bulala 20 kowannensu.

Kotun dai, wacce ta ke a ƙarƙashin Mai-shari’a Munzali Tanko ta yankewa samarin hukuncin ne sakamakon laifin shaye-shayen kayan maye.

Tun da fari dai, mutanen unguwar Mandawari da ke cikin birnin Kano ne su ka maka samarin a kotu sabo da sun addabe su da shaye-shaye.

Da ake tuhumar su a kan laifin da a ke zargin su, matasan sun amsa laifukan su.

Daga nan alƙalin bai yi wata-wata ba ya umarci dogarin kotu da ya tsatsala musu bulala ashirin kowannensu.

Bayan an gama yi musu bulalar ne sai Mai-shari’a Tanko ya yi musu nasiha da su zama mutanen kirki.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan