Mata sun gaza samun muƙami ko ɗaya a kwamitin shugabancin ƙungiyar ɗalibai a BUK

493

Sashin kula da jin daɗin ɗalibai na jami’ar Bayero da ke Kano, ya fitar da ƙunshin shugabancin kwamitin riƙo na ƙungiyar dalibai ta jami’ar na shekarar zangon karatu ta 2021/2022, da ake sa ran su ne za su jagoranci kungiyar ɗaliban.

Kwamitin riƙon ƙungiyar ɗaliban wanda ke ƙarƙashin shugabacin Sanata Auwal Lawal Nadabo da mataimakinsa Kwamared Ali Abdulkadir Adam, sai dai a cikin ƙunshin shugabancin kwamitin riƙon mai mutum goma sha biyar (15) babu mace ko ɗaya wanda hakan ya je fa alamar tambaya akan wannan tsari.

Kwamitin shugabancin ƙungiyar ɗalibai na jami’ar Bayero

Duk da cewa a wasu jami’o’in akan samu mace ta shugabanci ɗalibai domin ko a baya – bayan nan sai da aka rantsar da Kwamared Hauwa Sulaiman wacce aka fi sani da Jidder a matsayin shugabar ɗalibai ta jami’ar gwamnatin tarayya da ke garin Dutsinma, FUDMA a jihar Katsina, amma a wannan karon babu wakilcin ko mace ɗaya a ƙunshin shugabancin riƙon.

Jami’ar Bayero dai na ɗaya daga cikin manyan jami’o’in kasar nan wacce ta ke da yawan ɗalibai maza da mata, kuma jihar Kano ta kasance jiha ce da al’ummarta su ke adawa da bai wa mata damar samun muƙamai.

Wannan mataki da jami’ar Bayero ta ɗauka na zuwa a lokacin da masu rajin kare hakkin mata da kuma kungiyoyi a Najeriya ke kokawa kan abinda suka kira rashin damawa da matan yadda ya kamata a harkokin siyasa da na shugabanci.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan