Ni ba sa’anka bane, kaje ka yi duk abinda za ka yi – Sakon Buni ga Kabiru Marafa

829

Shugaban kwamitin rikon Jam’iyyar APC na kasa, gwamman jihar Yobe, Mai Mala Buni, yayi martani ga kalaman Sanata Kabiru Marafa, wanda ya zarge shi da kashe jam’iyyar APC, da kuma rashin cancantar rike mukamin shugaban jam’iyya don yana matsayin gwamna, har yace zai tafi kotu domin ayi masa fassara.

Mai Mala Buni ya bayyana hakan ne ta bakin kakakinsa, Mamman Mohammed, wanda ya bayyana cewa ruwa ne ya kare wa dan kada, shi yasa Marafa ya ke zubo maganganun da ba su da da kai bare gindi.

Mohammed ya ce kayar da Marafa da aka yi a zaben deliget da aka yi wanda ya fadi kasa warwas shine ya sa yake ta yi wa mutane kumfar baki ya na zazzaro ido wai za shi kotu, toh ” Ya sani shi karamin kwaro ne”.

”Ruwa ne ya kare wa dan kada, ta kare wa Marafa a siyasa. Da ga abu ya same shi sai ya ce wane ne yayi masa ba daidai ba. Maimakon karika watangaririya a gari kana ife-ife ka hutacce da kanka kawai ka rika garzaya wa kotu.”

Daga shafin Nasara Radio

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan