Rikicin APC A Kano: Yau Malam Ibrahim Shekarau zai gana da magoya bayansa

457

A yau Talata tsohon gwamnan jihar Kano, kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, za iyi wata ganawa ta musamman da magoya bayansa, musamman ƴan majalisar shura da tuntuɓa ta gidan siyasarsa, wato Advisory and Management Committee, da sauran magoya baya da ke ƙananan hukumomi 44 a fadin jihar Kano.

Taron zai gudana ne a fadar Sardaunan na Kano Sanata Shekarau da ke unguwar Mundubawa a Kano, da misalin karfe 10:00 na safe.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Senata Malam Ibrahim Shekarau

Tun a farkon watan Nuwambar nan ne dai rashin jituwar da ke tsakanin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamnan jihar, Senata Ibrahim Shekarau da wadansu jiga-jigan jam’iyyar, wanda har wa yau ƴan majalisar dattawa da majalisar wakilai ne daga jihar ta Kano ya yi ƙamari har ta kai ga haddasa rarrabuwar kai a zaben shugabanni na jihar da aka gudanar.

Wanda hakan ya haifar da shugabannin jam’iyyar APC biyu a Kano. Abdullahi Abbas na tsagin Ganduje da kuma Ahmadu Haruna Zago na tsagin Shekarau.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan