Zargin Satar Fasaha: Kamfanin Coca-cola ya maka Pop-cola a kotu

562

Kamfanin Coca-cola ya maka takwaransa na Mamuda Beverages Nigeria limited mai sarrafa lemon kwalbar nan na Pop-cola, a Babbar Kotun Kano kan zargin satar alamar kasuwancinsa.

Kano Focus ta ruwaito cewa, kamfanin Mamuda Beverages Nigeria limited ya ƙaddamar da lemon kwalba na Pop-cola ne a watan Yunin da ya gabata.

Tun da farko kwafin ƙarar da kamfanin na Coca Cola ya gabatar kotun ya yi ƙorafin yadda kamfani Mamuda Beverages ya saci fasahar zanen da ke jikin kwalbar Coca Cola, da a turance ake kira da RIBBON ya yi matuƙar kama da wanda ya ke jikin Coca Cola, tare kuma da kwaikwayon sunan na Coca Cola inda aka fitar da Pop-cola.

Haka kuma kamfanin na Coca Cola ya sanar da kotun cewa shi ke da haƙƙin mallakar sunansa tare da zanen na RIBBON a ciki da wajen Najeriya. Kamfanin ya ƙara da cewa waɗannan siffofi mallakin kuma sun yi amfani da su a kasashen duniya daban-daban ciki har da Najeriya.

Hakazalika kamfanin na Coca Cola ya buƙaci kotun da ta haramtawa kamfanin Pop-cola yin amfani da wadannan siffofi a manyam allunan talla da motocin da ke sufurin lemon Pop-cola, sakamakon yin amfani da siffofin da ba hakkin mallakarsa ba ne.

A nasa ɓangaren lauyan da ke kare kamfanin Mamuda Beverages,George Ogunyomi, ya buƙaci kotun da ta ba shi lokaci domin yin martani ga wannan ƙorafin satar fasaha da kamfanin ya yi musu.

A ƙarshe mai shari’a Muhammad Nasir – Yunusa ya ɗaga sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Disamba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan