Gorin ‘Asali’ ya sanya Jarumi Nuhu Abdullahi bajakolin takardunsa a shafin Facebook

18462

Mako guda da sashen Hausa na gidan rediyon BBC ya gudanar da wata tattaunawa ta musamman a cikin shirin ‘Daga Bakin Mai Ita’ da tauraron Kannywood Nuhu Abdullahi wanda aka fi sani da Mahmoud, inda tauraron ya amsa wasu tambayoyin da su ka shafi rayuwarsa da sana’arsa. Sai ga shi jarumin ya yi bajakolin takardunsa da su ka haɗa da na makarantar Firamare da na Sakandare da takardar shaidar karatun diploma da kuma takardar shaidar haihuwa.

Jarumi Nuhu Abdullahi ya yi wannan bajakolin ne a yau Laraba a shafinsa na facebook, biyo bayan wani mutum mai suna Ishaƙa Usman Wali da ya yi masa gorin mantawa da asalinsa.

Jarumi Nuhu Abdullahi

Tun da farko Ishaƙa Usman Wali ya yiwa jarumi Nuhu Abdullahi ƙorafi akan yadda ya ke gudun asalinsa a dalilin ɗaukakar da ya samu.

A cikin buɗaɗɗiyar wasikar da Ishaƙa Usman Wali ya aikewa da Nuhu Abdullahin wacce ta bazu a shafukan sadarwa na zamani tamkar wutar daji ya fara da cewa “Na yi matuƙar mamaki irin yadda na kalli hirarka da BBC HAUSA a shirinsu na DAGA BAKIN MAI ITA in da su ka so su ji tarihinka, Kai kuma sai ka nuna musu cewa an haifeka a garin Kano ka yi primary da secondary duk a jihar Kano. Hakika na ji babu daɗi sakamakon irin yadda na ga ka juyawa ƙauyenku baya saboda yanzu rayuwarka ta cigaba kuma na yi mamaki matuka“.

Jarumi Nuhu Abdullahi a lokacin yana dalibin Sakandare a Kano

Wannan dalilin ne ya sanya jarumin yin bajakolin takardunsa da su ka nuna cewa shi haifaffen unguwar Kawo ne da ke yankin ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Sai dai kuma jaridar Labarai24 ta fahimci jarumin ya goge wallafar takardun da ya yi da su ke nuna asalin shi haifaffen Kano ne. Amma daga baya jarumin ya yi wata gajeruwar nasiha ga matasa akan su gujewa munanan halaye tare kuma ƙauracewa dukkanin abin da ka iya ɓata musu lokaci.

Ga Nasihar da Jarumi Nuhu Abdullahi ya wallafa a shafinsa na facebook kamar haka:

Salam, kirana ga ƴan uwana matasa mu mai da hankali wurin ciyar da kan mu da wasunmu gaba mu daina ɓata lokaci akan abinda zai ɓata mana lokaci wanda bai da amfani. A ƴan shekaruna na samu cigaban da ko a mafarki ban yi zaton zan samu ba, amma Allah cikin ikon sa ya sa na samu. Mu zama masu jajircewa akan abinda ya ke gaskiya da kuma amana mu kuma guji ƙarya da sharri da hassada da ƙyashi, Allah sai ya taimake mu, wanda ya yi min wancan ƙaryar na yafe masa, kuma Allah ya shiryar da shi. Amin”

Nuhu Abdullahi

Gorin asali dai ba baƙon abu ba ne ga mutanen da su ka yi shuhura a wani ɓangare na rayuwa. Sai dai kuma a mafi yawan lokuta a birnin Kano akan yi wa mutum gorin cewa ba ɗan asalin birnin ba ne, inda akan jefe shi da kalmar ‘Bako’ ne ko kuma a danganta da shi da wata ƙabila ta daban.

Turawa Abokai

2 Sako

  1. Allah yasa mudace ameen ai ita dama nasara bata samuwa sai tayi karo da hassada fatanmu dai shine kawai Allah yasa mudace ameen

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan