Ko Me Ya Sa Farfesa Hafiz Abubakar Ya Bar Tafiyar Gandujiyya?

453

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya bar tafiyar Gabdujiyya inda ya koma ɓangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Farfesa Hafiz shi ne mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga 2015 zuwa 2018 lokacin da ya ajiye muƙamin domin yin takarar gwamna a jam’iyyar PDP.

Sai dai ya koma jam’iyyar PRP bayan ya gaza samun amincewar tsohon Gwamna, Rabiu Kwankwaso.

Daga baya kuma Farfesa Hafiz ya ƙara komawa APC Gandujiyya a 2019 bayan Gwamna Ganduje ya lashe zaɓe.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan