Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, tayi kira ga al’umma akan cewa suyi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa ta biyawa dalibai kudi don sakin sakamakon jarabawar kammala sikandire ta NECO, har dalibai sun gagara samun guraben karatu a manyan makarantu, inda gwamnatin tace ba haka zancen yake ba, sannan bai kamata a dinga sanya siyasa a harkokin ilimi ba.
Wata majiya da gidan redy Nasara ta bayyana cewa gwamnatin ta bayyana haka ne karkashin ma’aikatar ilimi ta jiha, cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kakakin ma’aikatar ilimi, Aliyu Yusuf, a madadin kwamishinan ilimi, Sanusi Muhammad Majidadin Kiru, da suka ce jinkirin ya samo asali ne tun a gwamnatin baya ta Kwankwaso, wacce ta gaza tare da soke daukar nauyin dalibai wajen rubuta jarabawar WAEC.
Jam’iyyar PDP ta bakin sakataren watsa labaranta na jihar Kano, Bashir Sanata, ya shaidawa Nasara Radio cewa, sun yi takaici akan yadda gwamnatin Kano ta janyowa dalibai asarar rashin samun gurbin karatu a bana, ya kuma ce ya kamata gwamnati ta samawa wadannan dalibai mafita, abinda ma’aikatar ilimin tace abin kunya ne ga jam’iyyar PDP, don bai kamata ta dinga yada labaran da ba na gaskiya bane.
Ma’aikatar ilimin tace, tana mai tabbatarwa dukkan al’umma cewa, ta karbi dukkan kudin da ya kamata daga gwamnatin jihar Kano, domin biyan wancan kudi ga hukumar jarabawar NECO, don a saki sakamakon daliban jihar Kano daga nan zuwa karshen makon da muke ciki, kuma ta tuntubi jami’ar Bayero Kano, jami’oi guda biyu mallakin gwamnatin jiha, da sauran manyan makarantu domin kara wa’adin bada gurbi (Admission) zuwa karshen wata Nuwamba.