Rashin iya jagorancin Ganduje ne silar rikicin APC a Kano – Ibrahim Shekarau

391

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya yi zargin cewa rashin iya jagorancin jam’iyya daga gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne silar rikicin da jam’iyyar APC ke fama da shi a jihar.

Sanata Shekarau ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da BBC a Kano jim kaɗan bayan kammala wani taron da ya yi da magoya bayansa kan halin da shugabancin jam’iyyar ta APC ke ciki a jihar da kaddamar da kwamitin majalisar shura ta gidan siyasarsa.

Shekarau ya zargi shugaban Jam’iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas da iƙirarin cewa APC a Kano ta Ganduje ce da mai ɗakinsa Gwaggo da kuma shi kansa Abdullahi Abbas ɗin.

Ya kuma ce an mayar da su saniyar ware a duk wasu al’amura na Kano kama daga batun taron jam’iyya zuwa sauran tarurruka da ba a rasa ba inda ya ce ba a ba su goron gayyata.

“Babu wani taro da aka gaya mini da ban je ba, kuma akwai abin da ake kira elders, me zai hana gwamna ya kira mu ya ce don Allah ina gani idan muka ba wane muna sha’awar ya yi ciyaman, idan da gyara za mu gyara maka, idan da wata illa za mu fada, idan babu illa za mu ce babu damuwa,” in ji shekarau.

Tsohon gwamna Shekarau ya ce ƙorafin da suka yi kan rikicin da ke tsakaninsu da ɓangaren Ganduje a yanzu yana gaban kwamitin sasanta rikicin APC na ƙasa wato kwamitin da su Abdullahi Adamu ke jagoranta.

“Majalisar shurar mu tana nan, yau shekara goma, amma shurar nan tana da alaƙa da siyasa abokan shawara ne na siyasa, sun san muna da tsari, gwamnati da ya yi zaɓen ƙananan hukumomi ya ƙare, amma dai zaɓen jam’iyya muna hakki.”

Rikicin da ke tsakanin ɓangaren Ganduje da na Shekarau a Kano ya yi sanadin rabuwar jam’iyyar gida biyu inda Ahmadu Haruna Zago jagorantar ɓangaren Shekarau sai kuma Abdullahi Abbas ɓangaren Ganduje.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan