Safiyya Daba ta lashe gasar ɗaukar hoto ta Equal Access

240

Safiyya Muhammad Daba ƴar jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta lashe gasar ɗaukar hoto da shahararriyar gidauniyar nan mai suna EQUAL ACCESS INTERNATIONAL ta shirya ta shekarar 2021.

Tun da farko an sanar da sunan Safiyyah Daba ne a matsayin wacce ta yi nasara a farkon watan Nuwamba, a lokacin wani taro da ya gudana a shafin intanet da gidauniyar Equal access din ta shirya.

Ba wannan dai karon farko da Safiyyah Daba ta lashe gasar ɗaukar hoto ba, domin ita ce yar Najeriya ɗaya tilo da lashe kyautar ɗaukar hoto ta African Women in Media (AWiM) ta shirya a shekarar 2021.

Safiyyah Muhammad Daba

Safiyyah Daba ta bayyana farin cikinta bisa wannan nasara da ta samu na lashe wannan gasa tare kuma da godewa Allah da kuma iyayenta.

“A gaskiya ban san abin da zan ce ba domin lashe wannan kyautar ya wuce tunanina. Ban taɓa tunanin cewa zan kasance cikin waɗanda suka yi nasara ba, har ma da wannan matsayi na farko”


“Ina godewa Allah da ya nuna min ranar da na samu damar ɗaukar hoton wani yaro a lokacin da ya ke ɗebo ruwa a kogi wanda shi ne dalilin nasarata”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan